Jam'iyyar Adawa ta PDP ta mayar da martani kan irin kalaman da ke fita daga bakin Sanatanta mafi girma a mulkin kasar nan, da cewa kalamai ne da basu dace ba.
Shi dai Sanatan yace a yadda al'amura ke tafiya yanzu, akwai yiwuwar sojoji su sake dawowa su kwaci mulki, kalamai da ake gani kamar yana ma gayyatar sojojin ne su zo su kori 'yan siyasa, bayan da binciken EFCC ya kai kansa kuma aka gano manyan kadarori kasashe daban-daban da aka ce wai nasa ne.
Jam'iyyar ta PDP, wadda tayi mulki tun 1999 zuwa 2015, bayan mulkin sojoji na kusan shekaru 30, tayi kira ga soji da kar su sake su saka rai da sake kwata ko mulkar Najeriya, da ma kiran lallai su yi zaman su a bariki, kuma su bi doka da oda su bar 'yan siyasa su mulki jama'a.
An dai dade ba'a ga juyin mulki ba, domin yanzu ya zama tsohon yayi, tunda kusan duk kasashen Afirka da a da ke karkashin soji yanzu sun koma na mulkin farar hulla.
Source :naij hausa
Title :
PDP Ta Maida Martani Kan Batun Juyin Mulkin Sojoji
Description : Jam'iyyar Adawa ta PDP ta mayar da martani kan irin kalaman da ke fita daga bakin Sanatanta mafi girma a mulkin kasar nan, da cewa kalam...
Rating :
5