Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun obasanjo ya bayyana rashin jin dadin sa game da yadda shugaba Muhammadu Buhari ya ki sanyawa takardar yarjejeniyar kasauwanci na bai-daya a nahiyar Afrika tare da fatan cewa zai sake shawara game da batub kafin lokaci ya kure.
Obasanjo yayi wannan tsokacin ne a yayin da yake jabakin sa a wajen wani taronshugabannin kamfanonin nahiyar a garin Abidjan, babban birnin kasar Cote d’Ivoire a ranar Talata da ta gabata.
Jaridar NAIJ ta samu cewa tsohon shugaban kasar na Najeriya ya bayyana cewa tabbas abun takaici ne yadda shugaba Buhari din ya ki sanyawa yarjejeriyar ta kasauwanci na bai-daya a nahiyar Afrika hannu domin a cewar sa tana da matukar anfani.
A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma babban dan siyasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam'iyyar APC ta basu kunya musamman ma ganin yadda suna yabon ta sallah amma sai gashi ta kasa alwalla.
Atiku din ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya jagoranci wasu jiga-jigan jam'iyyar ta sa ya zuwa gidan gwamnatin jihar Ribas a jiya inda aka ruwaito ya ayyana kudurin yin takarar shugaban kasa a 2019.
Source :naij hausa
Title :
Obasanjo Ya Sake Caccakar Buhari
Description : Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun obasanjo ya bayyana rashin jin dadin sa game da yadda shugaba Muhammadu Buhari ya ki sanyawa ta...
Rating :
5