A ranar Alhamis din nan ne data gabata Daya daga cikin masu neman kujerar shugaban kasar nan a karkashin inuwar jam'iyyar PDP kuma Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewar ba gaggawa yake ba akan burin sa na neman kujerar shugaban kasar nan, shi burin sa shine ya kawo wa al'ummar Najeriya cigaban da ya dace, sannan ya kara da cewa shine mutumin da zai iya gyara Najeriya.
Lamido yayi wannan sanarwar ne a yayin ganawar sa da shugabannin jam'iyyar PDP a babbar Sakatariyar jam'iyyar dake Sogunle a jihar Legas, yace ya yanke shawarar fitowa neman kujerar shugaban kasar ne saboda kokarin da yake dashi na ganin ya fitar da kasar nan daga halin da take ciki na rashin shugabancin daya dace.Lamido, wanda ya samu rakiyar tsohon ministan ayyuka na kasa, Mista Mike Onomalemen, da kuma sauran 'yan tawagar shi na yakin neman zabe, sannan kuma sunyi kira ga wakilan jam'iyyar PDP da su dubi cancanta a lokacin zaben fidda gwani a shekarar 2019.
A cewar Lamido tun lokacin da jam'iyyar PDP ta karbi mulki a shekarar 2015 har yanzu bata yi wani abin azo a gani ba, kullum kokarin ta shine ta dora laifin ta akan wanda suka yi mulki a baya.
A lokacin da tsohon gwamnan yake jawabi yace gwamnatin APC mai mulki ta kasa cika alkawuran data daukar wa kasar nan a lokacin yakin neman zabe a shekarar 2015, saboda haka dole ne mubi duk wata hanya domin kawar da jam'iyyar APC daga mulki.
Ya ce jam'iyyar APC babu abinda ta iya idan ba yada farfaganda ba.Sannan yayi misali da 'yan matan Dapchi wadanda 'yan ta'addar Boko Haram suka sace inda ya ce hakan yana kama da wasan kwaikwayo da gwamnatin nan take so tayi da yaran mu, sannan ya nuna hakan a matsayin gazawa na wannan gwamnatin APC. Sannan ya nemi 'yan jam'iyyar PDP dasu hada karfi da karfe domin ganin sun cire jam'iyyar APC daga mulki.
A karshe yayi godiya ga 'yan jam'iyyar PDP na jihar a bisa kokarin da suka yi wurin tarbar shi, sannan yayi godiya ga shugaban jam'iyyar PDP na jihar Legas a bisa kokarin daya nuna a wannan taron.
Source :naij hausa
Title :
Ni Kadaine Zan Iya Dawo Da Nijeriya Hayyacin Ta - Sule Lamido
Description : A ranar Alhamis din nan ne data gabata Daya daga cikin masu neman kujerar shugaban kasar nan a karkashin inuwar jam'iyyar PDP kuma Tsoho...
Rating :
5