Mun samu labari kwanan nan daga Rediyo Faransa cewa ya fara kukan barin tsohuwar Kungiyar sa ta Barcelona. 'Dan wasan da yanzu yake jinya yana kokarin komawa kulob din na sa na da. Wasu kuma na ganin dabara ce kurum.
Majiyar mu ta Jaridar Mundo Deportivo ta kasar Sifen ta bayyana mana cewa Babban Dan wasan gaban na PSG Neymar na kukan barin Lionel Messi da Barcelona inda yanzu ya fara tuntubar Kungiyar domin yayi kome.
Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Kungiyar Real Madrid ta yi waje da Kungiyar PSG daga Gasar UEFA ta Zakarun Nahiyar Turai. Yanzu haka dai 'Dan wasan gaban na Brazil ya na jinyar wani aiki ne da aka yi masa a kafa.
Yanzu duka dai ba wuce watanni 7 ba da 'Dan wasan ya kafa tarihi inda ya zama 'Dan wasa mafi tsada a Duniya bayan PSG ta saye sa daga Barcelona. Real Madrid dai a shirye ta ke ta kashe fam Miliyan 400 yanzu kan Tauraron.
Source :naij hausa
Title :
Neymar Na Neman Hanyar Da Zai Bar PSG
Description : Mun samu labari kwanan nan daga Rediyo Faransa cewa ya fara kukan barin tsohuwar Kungiyar sa ta Barcelona. 'Dan wasan da yanzu yake jiny...
Rating :
5