Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaidawa sakataren harakokin wajen Amurka Rex Tillerson matakan da gwamnatinsa ke dauka domin ceto 'yan matan Dapchi da Chibok
Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta zabi ta sasanta da Boko Haram maimakon yin amfani da karfin soja domin ceto 'yan matan a raye.
Wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adeshina ya fitar ta ce, Buhari ya shaidawa Mista Tillerson da ke ziyara a Najeriya cewa gwamnatinsa na aiki tare da wasu masu shiga tsakani da wasu kungiyoyin kasashen waje domin ceto 'yan matan ba tare wani abi ya same su ba.
A nasa bangaren sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya ce kasarsa na taka muhimmiyar rawa wajen ganin an ceto 'yan matan da mayakan Boko haram suka sace daga a makarantar garin Dapchi a Jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.
A yau Litinin ne sakataren harkokin wajen na Amurka Rex Tillerson ya isa Abuja babban birnin Najeriya, a ziyararsa ta farko zuwa kasar.
Mista Tillerson da Shugaba Muhammadu Buhari sun tattauna batutuwan da suka hada da na yaki da ta'addanci da batutuwan da suka shafi ayyukan jin kai a arewa maso gabashin Najeriya da kum tattalin arziki.
Ziyarar dai wani bangare ce ta rangadin da yake zuwa kasashen Afirka shida, da nufin tsaurara tsaro da kulla dangantakar kasuwanci.
A ziyarar ana ran za su amince a kan yadda za a kara samar da zaman lafiya da tsaro a yankin Naija Delta, da kuma gano hanyoyin da kasashen biyu za su amfana da juna ta fuskar kasuwanci da zuba jari.
Mista Tillerson dai yana ziyarar mako daya ne a Afirka.
Ya ziyarci yankin kusuwar Afirka kwanaki kadan bayan da ya sanar da bayar da sabon tallafi na dala miliyan 533 ga Afirka, inda a ciki aka ware dala miliyan 128 ga Najeriya da kasashen da suke makwabtaka da yankin Tafkin Chadi.
Ziyarar dai tana zuwa ne shekara guda bayan da Shugaba Donald Trump ya karbi mulki daga hannun Barack Obama.
Source :bbc hausa
Title :
Nafiso Na Sasanta Da Boko Haram Kan 'Yan Matan Dapchi - Buhari
Description : Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaidawa sakataren harakokin wajen Amurka Rex Tillerson matakan da gwamnatinsa ke dauka domin ceto ...
Rating :
5