Babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris yayi amai ya lashe game da batun kwashe Yansandan dake gadin attajirai a Najeriya, tare da dawo dasu hukumar don baiwa yan Najeriya tsaro.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito babban sufetan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 22 ga watan Maris, inda yace hukumar Yansanda ta dage kaddamar da wannan doka zuwa ranar 20 ga watan Afrilu.
Jaridar naij ta ruwaito a ranar 19 ga watan Maris ne rundunar Yansandan Najeriya ta sanar da janye jami’an Yansanda dake gadin masu kudi, yan siyasa da kamfanoni, sai dai a yanzu ta dakatar da batun don samun damar gudanar da aikin yadda ya kamata.
Kaakakin rundunar Yansandan Najeriya, Jimoh Moshood ne ya bayyana haka, inda yace an yanke wannan shawara ne bayan wata ganawa da Sufetan Yansandan yayi da kwamandojin Yansandan Moba, sashin yaki da ta’addanci da kuma sashin samar da tsaro na musamman, dukkaninsu na rundunar.
Jimoh yace wannan mataki da aka dauka zata baiwa hukumar damar duba yadda aka aika Yansandan zuwa inda suke aiki a yanzu tare da sanin hanyar da ta fi dacewa a janye su ba tare da karya doka ba.
Daga karshe Jimoh ya shawarci attajira, kamfanoni da yan siyasa da su cigaba da rike Yansandan dake gadinsu zuwa lokacin da rundunar Yansandan zata fitar da sabon umarni.
Source :naij hausa
Title :
Nafasa Janye Yan Sanda Daga Gadin Yan Siyasa - Sufeto Janar
Description : Babban sufetan Yansandan Najeriya, Ibrahim Idris yayi amai ya lashe game da batun kwashe Yansandan dake gadin attajirai a Najeriya, tare da ...
Rating :
5