Gwamanan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewar tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Kwankwaso, ya fi karuwa da shi domin ya sha daukan nauyin takarar Kwankwaso a baya.
A wata tattaunawa da gwaman ya yi da jaridar Sun, Ganduje ya yi waiwayen baya a kan yadda suka fara hulda da Kwankwaso tare da bayyana cewar ya fara siyasa ne tun Kwankwaso yana dalibi.Ganduje ya fito baro-baro ya bayyana cewar ba zata yiwu a ce sanata ne zai kasance jagoran jam'iyya dake da gwamna a jiha ba.
"Ta ya ya Sanata zai zama yana juya akalar jam'iyya a jiha bayan tana da gwamna a jihar? Ni fa ba dan dagajin siyasa kuma ba bako bane a cikinta. Lokacin da na fara siyasa, shi (Kwankwaso) yana makaranta kuma bayan shigowar sa siyasa na dauki nauyin takarar sa a matakai da dama," a kalaman gwamna Ganduje.
A dangane da sabanin siyasa da ya shiga tsakaninsu, Ganduje, ya ce anyi yunkurin sulhunta su sau 17 amma ba a yi nasara ba domin Kwankwaso ya shaidawa masu kokarin yi masu sulhu cewar shi da gwamna Ganduje yanzu ba abokan juna bane a saboda haka ba ya bukatar sulhuntawa da shi.
"Akwai lokacin da wasu gwamnoni suka so yi mana sulhu amma da suka bukaci ya zo gidan Mallam Aminu Kano a Abuja, sai ya ce ba zai zo ba. Na fada masu cewar ba damuwa, ni zan je mu same shi.
Mun je, mun same shi, mun tattauna ta tsawon lokaci har munyi musabiha amma koda yaushe cikin zagina yake bayan hakan," inji Ganduje.Ganduje ya yi waiwayen yadda a baya, tun lokacin yana darekta a Abuja, suke abota da Kwankwaso, tare da bayyana cewar har yanzu yana ganin girman Kwankwaso.
Saidai ya ce ba zata yiwu mutumin da yake matsayin Sanata ya ce zai ke juya akalar al'amuran siyasa da gwamnatin jiha ba.
Source :naij hausa
Title :
Nafara Siyasa Tun Kwankwaso Na Dan Karamin Dalibi - Ganduje
Description : Gwamanan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewar tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Kwankwaso, ya fi karuwa da shi domin ya...
Rating :
5