Dan kasuwar kasar Rasha, Sergei Mavrodi, da ya kirkiri tsarin MMM da ya talauta mutane da dama a kasar Rasha da Najeriya, ya mutu.
Mavrodi ya fara kirkirar tsarin MMM a shekarun 1990 kuma tun a wadancan shekarun ya damfari mutanen kasar Rasha kudi masu yawa ta hanyar tsarin.
Rahotanni sun bayyana cewar an garzaya da Mavrodi asibiti bayan ya yi korafi da ciwo a kirjinsa, sannan ya mutu bayan wasu wasu sa'o'i, kamar yadda kafar watsa labarai a kasar Rasha suka sanar.
An zabi Mavrodi a matsayin dan majalisa a shekarar 1994. Ya rasa kujerar sa a shekarar 1996.A shekarar 2007, wata kotu a birnin Moscow ta tabbatar da Mavrodi a matsayin dan cuwa-cuwa tare da yi masa hukunci.
A shekarar 2011, Mavrodi, ya kara bude tsarin MMM da ya kaddamar a kasashen India, China, Afrika ta kudu, Zimbabwe, da kuma Najeriya.
A duk kasashen, Mavrodi, ya rufe tsarin bayan jama'a sun narka kudi masu yawa cikin tsarin.
Source :naij hausa
Title :
Mutumin Daya Kirkiri Kamfanin MMM Ya Mutu
Description : Dan kasuwar kasar Rasha, Sergei Mavrodi, da ya kirkiri tsarin MMM da ya talauta mutane da dama a kasar Rasha da Najeriya, ya mutu. Mavrodi...
Rating :
5