Bayan sati biyu da mutuwar Sanata Ali Wakili daya daga cikin Sanatocin jihar Bauchi, akwai alamun cewar mutane sun fara tururuwa domin neman maye gurbin shi, tun lokacin da hukumar zabe ta kasa ta bada sanarwar cewar ana neman wanda zai maye gurbin shi a cikin kwana 90.
Sanata Wakili ya rasu a ranar 17 ga watan March 2018, an binne shi a Abuja, inda aka bada tsawon kwanaki uku domin zaman ta'aziyya a gidan sa dake jihar Bauchi.
A halin yanzu dai kusan sama da mutane 20 ne aka lissafa wadanda suke neman maye gurbin sa a majalisa, jam'iyyar APC mai mulki ita ta fitar da jerin mutanen, inda tace a halin yanzu an samu kimanin mutum 6 a karkashin jam'iyyar wadanda suka nuna sha'awar su akan kujerar ta shi.
Dokta Safiya Iliyasu ta kasance tun kafin mutuwar Sanata Ali Wakili ta nuna sha'awar ta akan kujerar a shekarar 2019.
Sannan akwai Barrister Lawan Ibrahim wanda yake mai bada shawara ga jam'iyyar APC, shi ma ya nuna kujerar dashi ta dace.Akwai kuma Ahmed Shu'aibu shima a karkashin jam'iyyar ta APC.
Sannan mun samu rahoton cewa tsohon gwamnan jihar Isa Yuguda, wanda Sanata Ali Wakili ya kada a zaben daya gabata shima ya nuna sha'awar shi akan kujerar.A jam'iyyar PDP kuwa akwai Garba Dahiru, Hajara Wanka da dai sauran mutane da yawa sun nuna sha'awar su akan kujerar.
Barrister Hussaini Umar, shima ya ce ba zai ayi wannan takara babu shi ba, inda ya fito a karkashin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP). Wanda ya jima yana kamfen na kujerar a shekarar 2019.
Masana a harkar siyasa sun bayyana cewar neman gurbin Wakilin ba zai zamo abu mai sauki ga manema kujerar ba, musamman ma da irin matsalar siyasa da ake samu a wannan lokacin a jihar Bauchi da kuma irin shirye - shiryen da ake yi na zaben 2019 a jihar .
Source :naij hausa
Title :
Mutanen Dake Zawarcin Kujerar Marigayi Sanata Ali Wakili
Description : Bayan sati biyu da mutuwar Sanata Ali Wakili daya daga cikin Sanatocin jihar Bauchi, akwai alamun cewar mutane sun fara tururuwa domin neman...
Rating :
5