Mun samu tabbacin cewa akalla mutum 90 su ka mutu a sanadiyyar cutar Lassa da ta kara dawowa Najeriya da wasu Yankin Afrika. Kawo yanzu dai Hukumar da ke kula da cututtuka tace sama da mutane 1000 sun kamu da cutar.
Hukumar ta NCDC ta kasar ta bayyana cewa zazzabin cutar Lassa tayi sanadiyyar rasa dinbin jama’a a cikin Jihohin Najeriya 18.
Yanzu haka cutar ta shiga Edo, Ondo, Bauchi, Nasarawa, Ebonyi, Anambra, Benuwe, Kogi, Imo, Filato, Legas, da ma Jihar Taraba.Kamar yadda mu ka samu labari har a Jihar Delta, da Osun, Ribas, Gombe, Ekiti.da Birnin Tarayya ana fama da wannan annoba.
Malaman asibiti kusan 14 su ka rasu a Johohin kasar. Ministan lafiya Isaac Adewole dai ya zargi Kwamishinonin lafiya da sakaci.
Yanzu Hukumar NCDC ta zuba Jami’ai a Iyakokin kasar domin hana cutar zagayawa. Kashi 21% na wanda su ka kamu da cutar dai su na rasuwa ne kamar yadda bincike ya nuna.
Malaman lafiya su na kira a zauna cikin tsabta domin gudun kamuwa da cutar.
Source :naij hausa
Title :
Mutane Fiye Da Dubu Sunkamu Da Cutar Lassa A Jahohi 18
Description : Mun samu tabbacin cewa akalla mutum 90 su ka mutu a sanadiyyar cutar Lassa da ta kara dawowa Najeriya da wasu Yankin Afrika. Kawo yanzu dai ...
Rating :
5