A wani bincike da hukumar kare hakkin bil adama tayi, ya nuna cewar, idan aka kwatanta da mabiya sauran addini a kasar Faransa, kasar ta fi tsana da nuna wariya ga addinin musulunci.
Kwamitin bincike na jaridar Le Monde wanda yake fitar da rahoto a kowacce shekara akan laifukan kyama da wariyar fata, jaridar ta ce rahoton wannan shekarar ya tabbatar da cewa ma'abota addinin musulunci suna fuskantar wariya, tsangwama da kyama fiye da kowanne addini a kasar Faransa.
A wani rahoton da jaridar ta fitar ta nuna a bangaren hare-hare da aka dinga kaiwa al'ummar musulmai kuma, hukumar leken asiri ta kasar Faransa ta bayyana cewa a shekarar data gabata sun samu rahoto har guda 72 wadanda keda alaka da kaiwa musulmai farmaki.
A wata kididdiga da jaridar ta Le Monde ta yi, ta nuna cewa kashi 44 cikin dari sun bayyana cewa addinin Musulunci barazana ce ga wayewar kasar ta Faransa, a yayin da kashi 61 cikin dari na al'ummar kasar suka nuna cewa saka Hijabi babbar matsala ce ga zaman lafiyar kasar.
Kasar ta Faransa wanda take da Musulmai kusan Milyan 4 wadanda mafi yawancin su 'yan Afrika ta Arewa ne, kasar ta kasance a sahun gaba a jadawalin kasashen da suka fi yawan Musulmai a yankin Turai.
Source :naij hausa
Title :
Musulunci Na Fuskantar Barazana A Kasar Faransa
Description : A wani bincike da hukumar kare hakkin bil adama tayi, ya nuna cewar, idan aka kwatanta da mabiya sauran addini a kasar Faransa, kasar ta fi ...
Rating :
5