Wani babban fasto a kasar Rasha, Smirnov Dmitri Nikolaevich, ya bayyana cewa al'ummar musulmai za su sake rike mulkin duniya, amma sai sun rike Alkur'ani hannu biyu-biyu.
Bishop din ya bayyana hakan a lokacin da yake bayani a wani gidan talabijin dake kasar, inda ya ce:
"Duk wani mai son ya fuskanci Islama, ya rungumi Alkur'ani mai girma ba wai Musulmi ba. Alkur'ani tsaftacacce ne babu karya ko zalunci a cikin sa, inda musulman yanzu babu wani abu da ya bambanta mu da su. Ba abinda aka rubuta a littafin a Alkur'ani suke aikatawa ba, yanzu yaudara, karya, zalunci da duk wani aikin sabo Musulmai suna aikatawa. Sai dai nayi imani da wani abu: Na tabbata cewa makomar duniya tana a Musulunci. Musulmai za su mulki duniya, idan har suka rungumi Alkur'ani hannu biyu."
Source :naij hausa
Title :
Musulmi Zasu Mulki Duniya Ne Kawai Da Taimakon Al Kur'ani-Pastor Smirnov Dmitri Nikolaevich
Description : Wani babban fasto a kasar Rasha, Smirnov Dmitri Nikolaevich, ya bayyana cewa al'ummar musulmai za su sake rike mulkin duniya, amma sai s...
Rating :
5