Gidauniyar Bill da Belinda Gates ta kashe tsabar kudi fiye da $1bn a Najeriya kamar yadda attajirin duniya Mr. Bill Gates ya bayyana a yayin da ya ziyarci Ministan Kudi na Najeriya, Kemi Adeosun a ofishin ta da ke Abuja.
Mr. Gates wanda ya kawo ziyarar aiki a Najeriya ya gana da ministan ne tare da wasu manyan jami'an gidauniyar na Bill and Belinda Gates.
A yayin da ya ke zaburar da gwamnatin tarayyah ta kara kwazo a fanin kula da lafiyar al'umma, ya kuma ce duk da makuddan kudaden da aka kashe wajen rigakafi a kasar, har yanzu akwai sauran rina a kaba.Ya ce akwai bukatar a sake yin nazari ga tsarin samar da lafiya a Najeriya don inganta shi.
Ya kara da cewa gidauniyar ta su da ma wasu masu ruwa da tsaki za su cigaba da taimakawa wajen samar da rigakafi a Najeriya na tsawon shekaru biyar zuwa goma nan gaba.
"Gidauniyar mu ta kashe fiye da $1bn a Najeriya, galibi a fannin samar da lafiya. Burin mu shine samar da cigaba a duniya baki daya.
Muna son mu tattauna yadda za mu rika samar da rigakafi da wasu ababe a fannin kiwon lafiya da kuma yadda cigaba da aiki tare," inji shi.
A jawabin ta, Ministan kudi Mrs. Adeosun ta ce Najeriya tana bayar da muhimmanci sosai wajen binciko hanyoyon magance matsalolin kiwon lafiya a kasar sai dai kuma kudaden harajin da ake biya a kasar ya yi kadan.
Ta kara da cewa gwamnatin za tayi kokarin daidaita harajin don samun kadaden da za'a yiwa al'umma aiki don hakan ya zama dole.
Source :naij hausa
Title :
Munkashe Fiye Da Dala Biyan Daya A Nijeriya - Bill Gate
Description : Gidauniyar Bill da Belinda Gates ta kashe tsabar kudi fiye da $1bn a Najeriya kamar yadda attajirin duniya Mr. Bill Gates ya bayyana a yayin...
Rating :
5