Shugaban rundunar sojin kasa ta kasa, Janar Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana cewar hukumar soji na kara yawan sansanin soji a fadin Najeriya domin dakile aiyukan ta'addanci.
Shugaban sojin ya bayyana haka ne yayin bikin bude wata sabuwar barikin soji a Elebele dake Yenagowa, babban birnin jihar Bayelsa.
Ya kara da cewar, shugaba Buhari, ba zai cinma manufar sa ta samar da tsaro ba muddin hukumar soji bata fadada aiyukan ta ba.
Ya bayyana cewar bude sansanin rundunar soji na 6 a Fatakwal da kuma ta 16 a Yenagowa na daga cikin aikin hukumar na fadada komar ta.
Buratai ya kara da cewar, ki a ranar 28 ga watan Fabrairu, saida ya ya halarci kaddamar da bude wata barikin soji a Katsina da kuma wata da aka gina a Monguno, jihar Borno, duk da ya ce za a mayar da shelkwatar ta jihar Sokoto da zarar zaman lafiya ya dawo yankin arewa maso gabas.
Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, da jami'an gwamnatin sa da kuma manyan dakarun soji ne su ka hakarci taron.
Source :naij hausa
Title :
Muna Kara Bazuwa A Kasannan Don Yaqi Da Yan Ta'adda-Buratai
Description : Shugaban rundunar sojin kasa ta kasa, Janar Tukur Yusuf Buratai, ya bayyana cewar hukumar soji na kara yawan sansanin soji a fadin Najeriya ...
Rating :
5