A jiya Sanatoci sun yi makokin marigayi Sanata Malam Ali Wakili wanda ya rasu a ranar Lahadi yana da shekaru 58 a duniya.Yan majalisan wadda suka yi zantutuka domin karrama Wakili a zangon majalisa, sun ce mutuwarsa darasi ne.
Wakili ya rasu ya bar matan aure biyu da yara goma tare da jikoki biyar.An daura tutar kasa da kan kujerar Wakili na majalisa. Sanatoci sun shafe sama da sa’o’’i biyu da rabi suna girmama dabi’un marigayin.
Ekweremadu ya ce: “Yana da matukar muhimmanci mu tambayi kawunanmu, wani darasi ne a cikin wannan dukka? Wannan darasi mai sauki shine komai zai zo karshe wata rana. Mulki, matsayi da dukannin sauran abubuwa zasu zo karshe.
”A baya jaridar naij ta kawo cewa aata babban tawaga da daga majalissar dattawan Najeriya karkashin jagorancin, Sanata Bukola, sun kai ziyarar ta’aziya ma Gwamnatin Bauchi Sarkin Bauchi da iyalin marigayi Ali Wakili akan mutuwar abokin su.
Source :naij hausa
Title :
Mun Koyi Darasi Daga Mutuwar Ali Wakili - Sanatoci
Description : A jiya Sanatoci sun yi makokin marigayi Sanata Malam Ali Wakili wanda ya rasu a ranar Lahadi yana da shekaru 58 a duniya.Yan majalisan wadda...
Rating :
5