Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce bai ga wanda yafi Magu Cancanta ya shugabanci hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ba duk da kasancewar har yanzu yana matsayin mai rikon kwarya ne bayan majalisar dattijai ta ki amincewa ta tantance shi.
Osinbajo na wadannan kalamai ne yayin wata hira da manema labarai da kuma ma’abota amfani da dandalin sada zumunta day a gudanar yayin wata ziyara day a kai jihar Legas a ranar juma’a ta makon day a wuce.
Mai taimakawa Osinbajo na musamman a kan watsa labarai, Laolu Akande, ya raba cikakkiyar hira ga manema Labarai a jiya, Talata, bayan raba wani bangare na hirar ranar Lahadi.
A cewar Osinbajo, babu abinda zai saka gwamnatin Buhari canja Magu daga shugabancin EFCC domin shine mafi cancanta duk da kasancewar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta aike da wani rahoto ga majalisar dattijai dake nuna rashin dacewar Magu da shugabancin hukumar EFCC.
Osinbajo y ace shugaba Buhari bay a katsalandan a harkokin hukumomin gwamnati, a saboda hakane ma ya ki saka baki cikin rahoton da DSS su ka aikewa majalisa.
Kazalika ya bayyana cewar majalisar dattijai nada nata ra’ayin kuma ba lallai ya zama daya da na fadar shugaban kasa ba.
Source :naij hausa
Title :
Mugune Yafi Cancanta Daya Rike EFCC-Osinbajo
Description : Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce bai ga wanda yafi Magu Cancanta ya shugabanci hukumar yaki da cin hanci da rashawa (E...
Rating :
5