Sanata Dino Melaye dake shan takaddama da rundunar Yansandan Najeriya da gwamnatin jihar Kogi ya tsallake Najeriya don ceton ransa, kamar yadda ya shaida ma gidan rediyon muryar Amurka.
Sanatan ya bayyana haka ne cikin wata hira da VOA Hausa ta yi da shi, inda yace ba zai daina sukar gwamnatin jihar Kogi da gwamnatin Najeriya ba don ta haka ne kawai za ayi gyara a Najeriya, har ma ya kara da cewa babu gudu babu ja daya, ko da kuwa za’a kashe shi ne.
“Wallahi tallahi! Wallahi tallahi!! Ba zan daina yi ma talakawan Najeriya yaki ba, ko da za’a kashe ni ne b azan bari ba, don da haka ne kadai za’a iya gyara Najeriya” Inji Sanata Dino Melaye.
Sai dai da majiyar jaridar naij ta tambaye shi meyasa ba zai gurfana a gaban Kotu ba, kamar yadda aka sa masa ranar 28 ga watan Maris, sai yace ba zai gurfana ba saboda babu wanda ya bashi sammaci, ko a jihar Kogi ko a Abuja.
Sanatan ya soki lamirin Yansanda da nufin kashe shi, inda yace: “Kotu ce kadai zata iya bada umarnin in gurfana gabanta, mai yasa Yansanda suke nemana inda ba nufin kashe ni suke yi ba? Sau hudu ana kokarin kashe ni fa, Kuma idan ban kare kai na ba, yakin da nake yi ma Talaka ma ai ba zai yiwu ba.
”Bugu da kari da aka tambaye shi yaushe zai koma Najeriya, sai Sanatan yace ba zai koma ba har sai ranar 20 ga watan Mayun shekarar 2019, inda ya cigaba da cewa tuni ya kai karar game da hare haren da aka kai masa zuwa ga majalisar dikin Duniya, UN, kasar Amurka, kungiyar Amnesty da kuma hukumar kare hakkin dan Adam na Najeriya.
Source :naij hausa
Title :
Melaye Yakai Karar Gwamnati Wa Majalisar Dinkin Duniya
Description : Sanata Dino Melaye dake shan takaddama da rundunar Yansandan Najeriya da gwamnatin jihar Kogi ya tsallake Najeriya don ceton ransa, kamar ya...
Rating :
5