Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 25 ga watan Maris ya gargadi yan Najeriya kan wasu mutane dake kokarin shirya masa makarkashiya domin bata masa suna.
Tsohon shugaban kasar, wanda ya shirya barin kasar zuwa Sierra Leone, ya yi wannan rubutu ne bayan wani zargi da ya bayyana a labarai cewa wani biloniya dake goyon bayansa ya yo hayan wasu mutane da suka saci bayanan lafiya da dukiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin zaben 2015.
Jonathan ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa: “An janyo hankalina kan cewa yayinda nayi tafiya domin bunkasa damokradiyya a kasar Sierra Leone, zaa gabatar da wani gangami domin bata mani suna ta hanyar amfani da mutanen da baa bayyana ba.
“A lokain da nake kan mulki nace kudirina bai cancanci zubar da jinin ko wani dan Najeriya ba. Ko lokacin da na bar mulki, na ci gaba da rikon haka.
“Abun da zan ce shine duk yadda karya ya kai ga tafiya cikin sauri, dole gaskiya zata sha gaban sa.”
Source :naij hausa
Title :
Matasa Suyi A Hankali Da Masu Kokarin Bata Musu Suna - Jonathan
Description : Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 25 ga watan Maris...
Rating :
5