Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewar zai baiwa matasa kashi 40 na mukaman gwamnatinsa, idan har ya zama shugaban kasar Najeriya a 2019, inji rahoton The Cables.
Majiyar jaridar naij ta ruwaito Atiku ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 25 ga watan Maris, a yayin kaddamar da shuwagabannin kasa da na jihohi a wata kwamitin bincike game da takarar Atikun.
Shugaban kungiyoyin goyon bayan Atiku, Oladimeji Fabiyi ne ya wakilici Atiku Abubakar, inda yace gwamnatin Atiku idan ta tabbata zata baiwa matasa kashi 40 na mukaman gwamnati sakamakon muhimmiyar rawar da suke takawa.
“Biyo bayan gano muhimmancin rawar da matasa ke takawa a wajen zabar shuwagabanni, na yi alkawarin basu kashi 40 na mukaman gwmanatina idan har na lashe zaben shugaban kasa na 2019.Don haka nake kira ga matasa da su bani goyon baya don cika musu wannan buri.” Inji Atiku.
Ita ma a nata jawabin, uwargidar shugaban kasar Najeriya, Titi Abubakar ta bayyana cewar Maigidanta, Atiku ne ya fi dacewa da zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP don zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 2019.
Titi, wanda ta samu wakilcin Sanata Grace Bent, ta bayyana cewar Atiku ne kadai ke da kwarewar kai jam’iyyar PDP ga nasara a zabukan na 2019.
Source :naij hausa
Title :
Matasa Ne Zasu Rike Kashi Arba'in Ba Mukaman Gwamnati Na- Atiku
Description : Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewar zai baiwa matasa kashi 40 na mukaman gwamnatinsa, idan har ya zama sh...
Rating :
5