Majalisar wakilai ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike game da yadda aka sace 'yan matan sakandaren garin Dapchi.
Kwamitin zai yi bincike ne kan yadda aka sace dalibai 'yan mata 110 a makarantar Dapchi da ke cikin jihar Yobe.
Dan Majalisa Goni Lawan daga Jihar Yobe wanda ya gabatar kudirin a majalisa, ya shaidawa BBC cewa kwamitin da aka kafa zai tafi garin Dapchi domin jajantawa iyayen yaran da aka sace tare da gudanar da bincike.
Ya ce kwamitin da Majalisa ta nada ya kunshi kwamitocin tsaro ne na majalisar da suka hada da na sojoji da 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
Kuma kwamitin zai yi aiki ne cikin mako hudu.
Nigeria: PDP ta nemi Buhari ya tafi Dapchi
Dapchi: Shin ba a koyi darasi ba ne daga Chibok?
Hon Goni ya ce aikin kwamitin ya shafi diba ta ina aka shiga aka fita lokacin da aka yi awon gaba da daliban. "Shin babu jami'an tsaro ne a lokacin?"
Wannan dai na zuwa ne bayan Gwamnatin shugaba Buhari ta kafa kwamitin mutane 12 domin gudanar da bincike kan yadda aka sace 'yan matan sakandaren na Dapchi.
Kwamitin na gwamnati ya kunshi sojojin kasa da na ruwa da na sama da kuma 'yan sanda da hukumar tsaro ta SSS da ta Civil defence.
Shi ma aikin kwamitin ya kunshi binciken dalilan da ke tattare da sace 'yan mata tare da fito da dubarun yadda za a gano su.
Sace 'yan matan dai ya haifar da rudani a Najeriya, inda sojoji da 'yan sanda ke sa-in-sa da juna kan wanda alhakin tsaron Dapchi ke kansa a lokacin da 'yan bindiga suka sace 'yan matan.
Source :bbc hausa
Title :
Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamitin Bincike A Dapchi
Description : Majalisar wakilai ta kafa kwamiti domin gudanar da bincike game da yadda aka sace 'yan matan sakandaren garin Dapchi. Kwamitin zai yi b...
Rating :
5