Majalisar dattijan Najeriya a jiya ta bayar da sanarwar aikawa da takardar sammaci zuwa ga shugaban dakarun sojin kasa na Najeriya Laftanal Janar Buratai da kuma Insifecta Janar na 'yan sandan Najeriya don su gurfana a gaban su.
Majalisar ta dattijai ta bayyana cewa wadanda ta kira din tana so su zo gabanta su yi mata cikakken bayani game da yadda aka yi aka sace 'yan matan makarantar kwanan nan na Dapchi har su 110 a watan da ya gabata.
A wani labarin kuma, Babbar hedikwatar sojin Najeriya dake garin Abuja ta fito ta nisanta kanta da kalaman mataimakin shugaban majalisar dattijan Najeriya Sanata Ike Ekweremadu game da yiwuwar afkuwar juyin mulki a kasar nan.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da hedikwatar ta fitar dauke da sa hannun mukaddashin mai magana da yawun ta Birgediya Janar J. A. Agim da aka fitar a jiya.
Source :naij hausa
Title :
Majalisar Dattijai Ta Aika Sammaci Wa Buratai Da Infecta Janar
Description : Majalisar dattijan Najeriya a jiya ta bayar da sanarwar aikawa da takardar sammaci zuwa ga shugaban dakarun sojin kasa na Najeriya Laftanal ...
Rating :
5