Tsohon gwamnan jihar Jigawa sannan dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido ya ce akwai lauje tattare da sace yan matan makarantar Dapchi da kuma sakin su wanda hakan a mayar da kasar Najeriya abun dariya a tsakanin kasashe.
Ya ce idan har aka bari jam’iyyar APC ta ci gaba da mulki a 2019, toh babu makawa zaa mayar da yan Najeriya shashashai.
Da yake magana a jihar Lagas, yayinda ya gana da tawagar PDP domin sanar masu da kudirinsa, Lamido a lura cewa APC bazata taba nasarar zaben 2019 ba.Ya samu tarba daga mambobin majalisar jihar karkashin jagorancin shugaba Hon.
Mashood Salvador da sauran yan majalisa.Lamido ya ce babu wani mai tunani da zai amince da al’amarin sace yan matan Dapchi.
A halin da ake ciki, mun samu wani karin haske daga Jaridar Daily Trust inda tayi dogon bayani game da yadda Gwamnati tayi namijin kokari wajen ceto 'Yan matan da aka sace kwanaki a Garin Dapchi a Jihar Yobe.Daga cikin abin da aka fahimta shi ne karshen Boko Haram ya karaso.
Yanzu dai Gwamnatin Buhari na kokarin hada kai da bangaren Boko Haram da ke karkashin Al-Barnawi domin ganin sun ajiye kayan aiki.
Sai dai zai yi matukar wahala a cin ma wannan matsala da mutanen bangaren Abubakar Shekau da su ka sace 'Yan matan Chibok.
Source :naij hausa
Title :
Maganan Satan Yan Matan Dapchi Rainin Hankali Ne - Sule Lamido
Description : Tsohon gwamnan jihar Jigawa sannan dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido ya ce akwai lauje tattare da sac...
Rating :
5