Wata mata, Leobogang Setshotloe, ta zargi likitan asibitin Moses Kotane, da karya hakarkarin jaririnta yayin karbar haihuwa.
Uwar 'yar kasar Afrika ta kudu ta bayyana cewar hukumomin asibitin sun hana ta ganin jaririyar ta na tsawon kwana guda, kafin daga bisani ta fuskanci cewar hakarkarin jariririyar ta a karye yake.
Setshotloe ta bayyanawa jaridar Sun cewar asibitin sun ci amanar ta.
"Na tambayi ma'aikaciyar asibitin abinda ya sa hakarkarin jariririyar take a karye, amma sai kawai ta ce min likitan ya yi nadamar abinda ya faru, wai kuskure ne," a cewar Setshotloe.Sannan ta cigaba da cewa "ban yarda da abin da ta fadamin ba don kamata ya yi likitan ya sanar da ni da kan sa, sannan ya nemi gafara a wuri na.
"Uwar ta bayyana cewar abinda ya faru ya matukar bata mata rai, saboda haka tana bukatar likitan da hukumar asibitin su nemi afuwar ta.Wani kawun matar, Jacob Kobedi, ya ce ba zasu yarda da abin da likitan ya aikata ba, a saboda haka zasu bi hakkin su.
Kakakin ma'aikatar lafiya a yankin arewa maso yamma na kasar Afrika ta kudu, Tebogo Lekgethwane, ya ce suna gudanar da bincike a kan wannan zargi da matar ke yiwa likitan.
Source :naij hausa
Title :
Likita Ya Karya Hakarkarin Jariri Yayin Karban Haihuwa
Description : Wata mata, Leobogang Setshotloe, ta zargi likitan asibitin Moses Kotane, da karya hakarkarin jaririnta yayin karbar haihuwa. Uwar 'yar ...
Rating :
5