Bisa dukkan alamu dai tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanatan Jihar a yanzu watau Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso zai nemi takarar Shugaban kasar nan ba da dadewa ba.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya nuna da gaske yake yi wajen neman kujerar Shugaban kasa bayan da ya bude shafukan sadarwa na zamani irin su Tuwita da Facebook kwanan nan. Ba mamaki Sanatan ya fara shirin kamfe ne.
Jagoran na Kwankwasiyya yayi wannan yunkuri wajen shirin takarar Shugaban kasa bayan da ya nemi jama'a su biyo shi a shafukan na sa. Kusan dai shi ma Shugaban kasa Buhari da haka ga fara kafin ya samu nasara a zaben 2015.
Sai dai wasu har sun fara nuna cewa tsohon Gwamnan yayi makarar fara amfani da irin wadannan kafofin na zamani kuma hakan nuna cewa za a ga tafiyar hawainiya idan yayi mulki. Har yau dai bai nuna niyyar sa ba a fili.
Source :naij hausa
Title :
Kwankwaso Yaqara Yunkurin Zamowa Shugaban Kasa
Description : Bisa dukkan alamu dai tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanatan Jihar a yanzu watau Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso zai nemi takarar Shugaban kas...
Rating :
5