Rundunar 'yan sanda jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce, kawo yanzu bayanai sun tabbatar da mutuwar mutum 10 sakamakon rikicin kabilanci da ya barke kwanaki uku da suka gabata a yankin karamar hukumar Sardauna.
To sai dai yayin da 'yan sandan ke cewa sun riga sun shawo kan matsalar, wasu kuwa na cewa ana ci gaba da yi musu kisan mummuke har yammacin ranar Lahadi, kamar yadda wani mazaunin kauyen Nyiwa da ke mazabar Wuro-gagarau ta karamar hukumar Sardaunar ya shaida wa BBC.
Sai dai BBC ta yi jin ta bakin 'yan kabilar Mambila amma hakan bai samu ba har zuwa lokacin wallafa wannan labari.
To sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta Taraba ta ce ba kamar yadda Fulani suka yi ikirari ba, rikicin ya shafi kabilun biyu wato na Fulani da Mambila kamar yadda kakakin rundunar, David Misal ya shaida wa BBC.
A watan Yunin da ya gabata ma dai an samu irin wannan rikici inda har kungiyar fulani ta Miyetti Allah ta yi zargin cewa an kashe fulani sama da 800 a wani hari da aka kai musu garin na Mambila.
Wasu dai na ganin cewa, ana ci gaba da samun rikicin ne saboda rashin daukar mataki a kan mutanen da ake zargi da haddasa rikicin.
Source :bbc hausa
Title :
Kunsan Adadin Mutanen Da Aka Kashe A Mambila?
Description : Rundunar 'yan sanda jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce, kawo yanzu bayanai sun tabbatar da mutuwar mutum 10 sakamakon...
Rating :
5