Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai yayi tir ga yadda kungiyoyin ma'aikata ke gudanar da harkokin su a Najeriya, ya na cewa barnar da sukeyi a kasar ya dara gudunmuwar da suka bayar wa.
El-Rufai ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, a garin Abuja wajen wani taron Inganta ayyukan gwamnati da wata kungiya mai suna 'Development Alternative Incorporation (DAI) ta shirya.
"Kungiyoyin ma'aikatan basu yi ma kasar wani aikin kirki ba. Sun kasance masu son kai kuma komai ya kasance akan dan karamin tunaninsu ne. Gaba daya, a Najeriya kungiyoyin cinikayya sun kasance hadari ga ci gabanmu kuma ina ganin ya kamata a taka musu birki.
"Ina tunanin kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya sun kasance mafi rashin sanin ya kamata, saboda in ba Likitan da bai san ya kamata ba, ta yaya zai tafi ya bar mara lafiya bayan yayi rantsuwa dama ta yaudara. Ina tunanin Likitocin Najeriya ne kadai a duniya ke tafiya yajin aiki.
"Mun mika korafinmu game da aikin gwamnatin na gaskiya, kuma za’a kaishi ga Majalissar Dokoki. Muna fata Majalissar Dokokin kasar za ta dakatar da duk wata matsala dake gabanta domin magance matsaloli na gaskiya," inji shi.
Source :naij hausa
Title :
Kungiyoyin Ma'aikata Nakawo Cikas Wa Ci Gaban Kasarnan-El Rufa'i
Description : Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai yayi tir ga yadda kungiyoyin ma'aikata ke gudanar da harkokin su a Najeriya, ya na cewa barn...
Rating :
5