Wani tsohon jami’in gwamnatin Najeriya da ya wawushe kudin yan fansho na jami’an Yansandan Najeriya da suka yi ritaya, John Yusuf ya gamu da hukunci mai tsauri da ya dace da shi.
Jaridar naij ta ruwaito kimanin shekaru biyar da suka gabata ne dai wata Kotu ta yanke ma John hukunci mai sassauci, sai dai hukumar EFCC ta dage sauraron karar zuwa Kotun daukaka kara dake babban birnin tarayya Abuja.
Hukuncin da kotun baya ta yanke ma John, wanda hukumar EFCC ke ganin hakan ba adalci bane, shi ne ta yanke masa hukucin zaman gidan Kurkuku na tsawon shekaru biyu ko kuma ya biya tara na naira dubu 750.
A zaman kotun na ranar Laraba 21 ga watan Maris ne Alkalan Kotun suka yanke ma barawon hukuncin daurin shekaru shidda a gidan Yari, tare da umartarsa da dawo da kudi naira biliyan 22.9.
Sai dai shima wand aake tuhuma John Yusuf ya amsa dukkanin tuhume tuhumen da ake yi masa, inda yace ya san dai ya wawushe naira biliyan 24 daga kudaden fansho na Yansandan Najeriya, don amfanin kashin kansa.
Source :naij hausa
Title :
Kotu Tayanke Wa Barawon Kudin Yan Fansho Shekara 6 A Gidan Yari
Description : Wani tsohon jami’in gwamnatin Najeriya da ya wawushe kudin yan fansho na jami’an Yansandan Najeriya da suka yi ritaya, John Yusuf ya gamu da...
Rating :
5