Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja baban birnin Najeriya ta bayar da belin Maryam Sanda wadda ake zargi da akshe mijinta, Bilyamin Bello a watan oktobar shekarar da ta gabata.
Alkalin kotun Haliru Bello ne ya bayar da belin Maryam a ranar Laraba bisa hujjar yanayin lafiyarta.
Bayan kammala saurraon shari'ar ta ranar Laraba, lauyoyin Maryam sun shaida wa manema labarai cewa Maryam tana fama da ciwon asma, don haka yanayin gidan yari da aka kulle ta a Suleja na iya kara ta'azzara rashin lafiyar tata.
A don haka ne Mai shari'a Bello ya bayar da belin nata saboda 'yan sanda sun kasa gabatar da kwararan hujjojin da ke nuna cewa gidan yarin Sulejan yana da ingantaccen tsarin da za a iya kula da ita da lalurarta.
Sai dai kotun ta bayar da belin ne bisa sharadin sai Maryam din ta gabatar da mutum biyu da za su tsaya mata, wadanda suka mallaki gida a Abuja, inda za su bayar da takardun gidan.
Haka kuma kotun ta bukaci mahaifin Maryam din ya sanya hannu a wata takarda don yin alkawarin cewa zai dinga kai ta kotun a duk lokacin da za a yi zaman sauraron kara.
An daga shari'ar zuwa ranar 19 ga watan Maris don ci gaba da sauraron karar.
Maryam Sanda 'na da cikin wata uku'
An kai wadda ake zargi da kashe mijinta gidan yari a Abuja
An fara binciken matar da ake zargi ta daɓa wa mijinta wuka a Abuja
Dama tun a watan Fabrairun da ya gabata lauyoyin Maryam suka bukaci a bayar da belinta domin ta je ta yi 'goyon cikin wata uku da take dauke da shi'.
Lauyanta, Joseph Daudu (SAN) ya shaida wa kotun da ke Abuja, cewa ci gaba tsare Maryam a gidan yari ka iya yin illa ga jaririn da ke cikinta.
Kalli yadda aka gurfanar da Maryam Sanda da 'yan uwanta
Ya kara da cewa bai taba ganin wani hukuncin kotu da ya amince a tsare macen da ke dauke da juna biyu ba sakamakon aikata laifi komai girmansa.
An fara gurfanar da Maryam a gaban kotu ne a watan Nuwambar 2018 bisa zarginta da kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka.
Rundunar 'yan sandan Najeriya wadda ta shigar da karar ta ce ana tuhumar Maryam da laifin ne a karkashin dokar kundin hukunta laifuka ta Najeriya sashe na 221.
Source :bbc hausa
Title :
Kotu Ta Bayar Da Belin Wacce Ake Zargin Takashe Mijinta Wato Maryam Sanda
Description : Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja baban birnin Najeriya ta bayar da belin Maryam Sanda wadda ake zargi da akshe mijinta, Bilyamin Bello ...
Rating :
5