Babbar abokiyar hamayyar Koriya ta arewa kuma makwafciyar ta watau Koriya Ta Kudu ta ce shugaban Koriya Ta Arewa, Kim Jong-un ya bayar da hasken cewa zai so hawa teburin tattaunawa a kan rabuwa da makaman nukiliya idan za a ba shi tabbacin tsaron kasarsa.
Kasar ta Koriya Ta Kudun ta ce dai an tattauna wannan batun ne a yayin da wasu wakilan ta suka gana da shugaban na Koriya Ta Arewa mai suna Kim Jong-un a birnin Pyongyang babban birnin kasar a ranar Litinin din da ta gabata.
Jaridar naij haka zalika ta samu cewa gwamnatin ta Kasar ta Koriya Ta Kudun a birnin Seoul ta kuma bayyana cewa Koriya Ta Arewa ta ce a shirye take ta gudanar da tattaunawa da Amurka game da dakatar da gwaje-gwajenta na makamai masu linzami da na nukiliya.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a can baya kasar ta Koriya Ta Arewa ta sha yin fatali da alkawuran da take dauka na dakatar da shirin nukiliyarta.
Source :naij hausa
Title :
Kim Jong-Un Yabada Sharudan Rabuwa Da Makamansa
Description : Babbar abokiyar hamayyar Koriya ta arewa kuma makwafciyar ta watau Koriya Ta Kudu ta ce shugaban Koriya Ta Arewa, Kim Jong-un ya bayar da ha...
Rating :
5