Gwamnatin kasar Birtaniya ta bayyana cewar bata da matsala da burin shugaban kasa Muhammadu Buhari na sake tsayawa takarar shugaban kasa karo na biyu a zabukan 2019, inji rahoton Premium Times.
Jakadan kasar Birtaniya, Paul Arkwright ne ya bayyana haka ga majiyar NAIJ.com, inda yace ba ma kasar Birtaniya kadai ba, hatta sauran kasashen Turai basu da matsala da sake tsayawa takarar Buhari.
“Ba kamar yadda ake yayatawa ba na cewa wai Birtaniya bata son Buhari ya sake tsayawa takara ba, Ina tabbatar muku wannan jita jita ne, kuma na ji dadin karyata hakan, kasar Birtaniya na son Najeriya ta bi tsarin fitar da shugaba, wanda yan Najeriya zasu zaba da kansu.” Inji shi.
Sai dai har zuwa yanzu Buhari bai sanar da burinsa na tsayawa takara ba karara, amma akwai alamu da dama da suka nuna yana sunsunan sake tsayawa takarar, kamar yadda ake gani tare da shi ko hadimansa.
Jakadan ya kara da cewa: “Ya kamata yan Najeriya su sani cewa suna da muhimmiyar rawa da zasu taka a tsarin dimukradiyya, don haka kowa yaje ya amsa katinsa na zabe, Birtaniya bata da wani dan takara, yan Najeriya ne zasu zabi wanda suke so.
”Daga karshe kuma yace kasar Birtaniya na aiki hannu da hannu da hukumar zabe mai zaman kanta, INEC don tabbatar da ingantacce zabe a shekarar 2019.
Source :naij hausa
Title :
Kasar Birtaniya Ta Mara Wa Buhari Baya Ya Sake Neman Takara
Description : Gwamnatin kasar Birtaniya ta bayyana cewar bata da matsala da burin shugaban kasa Muhammadu Buhari na sake tsayawa takarar shugaban kasa kar...
Rating :
5