Dan uwan marigayi Martin Luther King Jr, Isaac newton-Farris Jnr, ya yi kira gay an Najeriya da su bada hadin kai da shugaba Muhammadu Buhari wajen karashe ayyukan da ya fara domin gina Najeriya.
Farris ya bayyana hakan ne a wani hira da manema labarai a Abuja bayan ganawarsa da shugaba Buhari a wani liyafa da aka shirya musu a fadar shugaban kasa.
Yace: “Shawarana ga yan Najeriya shine, na san yadda yan Najeriya ke ji, ba su dadin shugaba Buhari yadda yake gudanar da abubuwa cikin sanyi.
“Ina baiwa yan Najeriya shawara su baiwa wannan bawan Allah lokaci domin yin aikin da yake yi. Shine shugaba mafi ingancin da wannan nahiya ta taba samarwa.“Ina baku tabbacin cewa idan kuka rike shi, zai mayar da Najeriya wuri alfahari.
”“Kun san mutumin kirki ne amma idan kukayi tunanin zai dinga amfani da karfinsa wajen ladabta masu rashawa ba tare da bin doka ba, mai zai faru idan wani mara mutunci ya zama shugaba gobe?”
Source :naij hausa
Title :
Karkuyi Watsi Da Buhari, Mutumin Arziki Ne - Dan Uwan Martin Luther King
Description : Dan uwan marigayi Martin Luther King Jr, Isaac newton-Farris Jnr, ya yi kira gay an Najeriya da su bada hadin kai da shugaba Muhammadu Buhar...
Rating :
5