Dan Majalisan Dattawa Gudaji Muhammad Kazaure ya gargadi sauran abokan aikin sa na Majalisar kan bawa mata yanci da daura su kan karagar mulki Najeriya.
Dan Majalisar mai wakiltan yankunnan Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankawashi na jihar Jigawa ya ce duk lokacin da aka bawa mata yanci da yawa, sukan kwace mulkin ne gaba daya daga hannun mazan saboda kaifin basirar su.
A jawabin sa na muranar ranar mata na duniya, Kazaure ya ce "Yana da kyau a karfafa wa mata gwiwa a harkar siyasa da kasuwanci saboda irin rawar da suke takawa a rayuwar mu.
"Amma abin da nake tsoro shine matan fa sune ke mulkar mazajen su a gida, idan aka basu yanci sosai a waje, za su mamaye ko ina.
"Idan aka basu yanci sosai, wata rana zasu hambare mazar. Muna iya zuwa Majalisar mu tarar muta sun mamaye ko ina kuma abubuwa ba za su tafi daidai ba saboda suna da basira sosai," inji shi.Kazaure ya yi wannan jawabin ne a ranar da aka ware don murnar zagayowar mata na duniya.
Danlami kurfi ya ce tallafin da ya bawa matan ya lashe kudi naira miliyan 30 kuma an rabar ne ga mata daga garuruwan da ke karkashin yankunan da yake wakilta.
Source :naij hausa
Title :
Kar Abawa Mata Yanci Sosai-Gudaji Kazaure
Description : Dan Majalisan Dattawa Gudaji Muhammad Kazaure ya gargadi sauran abokan aikin sa na Majalisar kan bawa mata yanci da daura su kan karagar mul...
Rating :
5