Sama da mutane 100,000 ne a jihar Adamawa suka bar jam'iyyar PDP da APC mai mulki suka koma sabuwar jam'iyyar SDP.
Shugaban jam'iyyar SDP, Cif Olu Falae, shi ya sanar da hakan a jiya lokacin da jam'iyyar ta ke bikin karbar Cif Emmanuel Bello, wanda yayi kaura ya dawo jam'iyyar jiya a garin Yola.
"Na zo na karbi Cif Emmanuel Bello da kuma mutane 100,000 wanda suka canja sheka daga jam'iyyar APC mai mulki da kuma jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar mu mai albarka ta SDP, daga yau sun zama cikakkun 'yan jam'iyyar SDP," inji shugaban jam'iyyar.
Ya ce jam'iyyar SDP ta jima a kasar nan, jam'iyyar ta yi shiru ne tun lokacin da marigayi Abiola da Babagana Kingibe suka barta a shekarar 1993.
Shugaban jam'iyyar na kasa, Farfesa Jerry Gana, ya ce wannan ita ce fita ta farko da suka yi a wannan shekarar, inda ya kara da cewar jam'iyyar tana maraba da duk wanda yake sha'awar shigowa cikin ta.
Source :naij hausa
Title :
Jam'iyyar SDP Ta Kwashe Sama Da Mutum 100,00 Daga Jam'iyyar PDP Da APC
Description : Sama da mutane 100,000 ne a jihar Adamawa suka bar jam'iyyar PDP da APC mai mulki suka koma sabuwar jam'iyyar SDP. Shugaban jam...
Rating :
5