Sanannar jarumar nan kuma shahararriya a masana'antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood da kuma na fina-finan kudancin kasar nan watau Nollywood mai suna Rahama Sadau ta yi karin haske game da wanda ta ke so ta aure nan ba da dadewa ba.
Jarumar dai ta yi wannan bayanin ne yayin da take fira da wakilin majiyar mu a farkon wannan watan lokacin da ya tambaye ta ko ta taba yin aure a rayuwar ta.
Yayin bada ansar ta ta dai jarumar dariya ta yi sannan ta bayyana cewa bata taba yin aure ba amma ta kusa in Allah ya so, kamar dai yadda ta ce.
Haka zalika a wakilin majiyar ta mu ya tambaye ta ko wanene masoyin nata kuma ko yana yin harkar fim ko ko ba ya yi sai jarumar ta yi togacciya ta bayyana cewa ba za ta iya sanar da sunan na sa ba a yanzu amma kuma sai ta tabbatar da cewa ba ya yin fim.
Da aka tambayi jarumar kuma ko meye alakar ta da Ali Nuhu musamman ma yadda jama'a ke danganta su da cewa su masoya ne, sai ta ce wannan maganar ba gaskiya bace domin ita Ali Nuhu yayana ne kuma ubangidana a wurin ta.
Daga karshe kuma sai jarumar ta bayyana cewa dukkan mace za ta so ta auri namiji irin Ali Nuhu din musamman ma saboda mutum ne nagari, mai tausayi da kyautatawa wanda kuma sune siffofin da duk wata mace ke nema.
Source :naij hausa
Title :
Irin Mutumin Da Zan Aura - Rahma Sadau
Description : Sanannar jarumar nan kuma shahararriya a masana'antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood da kuma na fina-finan kudancin kasar nan wata...
Rating :
5