Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) ta fitar da jadawalin cigaba da yiwa Sanata Dino Melaye kiranye. Mr. Melaye dan majalisa ne mai wakiltan yankin Kogi ta yamma a majalisar ta dattawa.
Sanarwan fitar da rannakun da za'a gabatar da kiranyen ya fito ne ta hannun sakataren hukumar ta INEC, Augusta Ogakwu a jiya Juma'a.
Kamar yadda jidawalin kiranyen ya bayyana, za'a fara ne da baza sanarwan tattancewa a ofishin hukumar da ke karamar hukumar Lokoja babban birnin jihar ta Kogi a ranar 27 ga watan Maris.
Hakazalika, za'a rufe karaban takardun masu sa ido kan kiranyen a ranar 4 ga watan Afrilu a hedkwatan hukumar da ke babban birnin tarayya Abuja.A ranar 25 ga watan Afrilu, za'a gudanar da taron masu ruwa da tsaki game da kiranyen a ofishin INEC da ke jihar.
Za'a jefa kuri'a na yi masa kiranye ko akasin haka a ranar 28 na watan Afrilu, sannan za'a sanar da sakamakon kuri'ar da al'ummar uankin nasa suka kada a ranar 29 ga watan Afrilu na 2018
Source :naij hausa
Title :
INEC Ta Fitar Da Jadawalin Kiranyen Dino Melaye
Description : Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) ta fitar da jadawalin cigaba da yiwa Sanata Dino Melaye kiranye. Mr. Melaye dan majalisa ne mai ...
Rating :
5