Wani sabon bincike ya bayyana cewa, girman ta'ammali da ake yi da igiyar leko a nahiyyar Afirka, Asia da kuma Amurka ta Kudu ya kai wani munzali wanda kafin a kaurace sai an dauki tsawon lokaci.
Mafi akasarin mutane ba su da masaniya akan illar da igiyar leko ke yiwa hunhu na dan Adam. Wannan illa ta maganin Sauro ta zarce irin illar da hayaki na karan sigari keyi.
Sandeep Salvi, shugaban cibiyar binciken lafiya kirji ta Chest Research Foundation ya bayyana cewa, kone igiyar leko guda daya ya kan saki kwayoyin cuta na formaldehyde da sai an kone kararen sigari 51 kafin su goga kafada da na igiyar leko.
Binciken ya tabbatar da cewa, kone igiyar leko guda daya ta kan saki kwayoyi cuta da sai an kone kararen 75 zuwa 137 a bisa ma'aunin gram.
Source :naij hausa
Title :
Illar Igiyar Leko A Jikin Dan Adam Yafi Na Sigari
Description : Wani sabon bincike ya bayyana cewa, girman ta'ammali da ake yi da igiyar leko a nahiyyar Afirka, Asia da kuma Amurka ta Kudu ya kai wani...
Rating :
5