Kasancewar Shinkafa ta zamto gama-gari a fadin duniya, domin kuwa abu ne mai wuya a rasata a gidan Talaka da mai kudi sakamakon yadda al'ummar duniya suka kafa mata kahon zuka na ta'ammali da ita kusan kowace rana zata hudo kai.
Wani sabon bincike da aka gudanar a jami'ar Havard ta kasar Amurka ya bayyana cewa, da yawan mutane masu ta'ammali da shinkafa a koda yaushe suna yiwa lafiyar jikin su barazana da cutar ciwon suga da a turance ake kiran ta type-2 diabetes.
Akwai wasu binciken kuma da aka gudanar a kasashen Sin, Japan, Amurka da Australia kan mutane 352, 000 da basu dauke da cutar ta ciwon suga, inda bayan an dora su kan ta'ammali da shinkafa na tsawon shekaru 4 zuwa 22 cutar ta fara bayyana jikin su.
Wani kwararren likita Dakta Qi Sun ya bayyana cewa, barazanar ciwon suga ta fi karfi ga masu ta'ammali da farar shinkafa sabanin jar shinkafa, wadda hasali ma ta kunshi wasu sunadarai na karin lafiya kamar Magnesium, Vitamins, Fiber da makamantan su.
Baya ga cutar ciwon suga, wani sabon bincike da aka gudanar a shekarar da ta gabata ya bayyana cewa, shinkafa tana tattare da wani sunadarin Arsenic wanda ke da nasaba da cutar daji wato kansa.
Jaridar NAIJ.com ta kuma ruwiato cewa, dalibai 1, 700 za su zana jarrabawar neman shiga jami'a a jihar Borno yayin da aka cafke wasu tagwaye da magudi yayin jarrabawar a ranar Juma'ar da ta gabata.
Source :naij hausa
Title :
Illar Da Shinkafa Keyiwa Lafiyar Dan Adam
Description : Kasancewar Shinkafa ta zamto gama-gari a fadin duniya, domin kuwa abu ne mai wuya a rasata a gidan Talaka da mai kudi sakamakon yadda al...
Rating :
5