Jiragen alfarma na shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari guda biyu da yayi alkawarin sayarwa domin tattalin kudin kasa na Falcon 7X da kuma Hawker 4000 har yanzu suna nan, kamar dai yadda binciken wata majiyar mu ta tabbatar.
Sai dai kamar yadda muke samu, fadar shugaban kasar ta bayyana cewa masu sayen jiragen ne suka yi masu tayin banza shine ma kuma babban dalilin da yasa har yanzu ba a saida su ba.
Jaridar Naij haka zalika ta samu cewa mai magana da yawun shugaban kasar, Muhammadu Buhari watau Garba Shehu ya bayyana cewa a tun farko dai an kiyasta cewa za'a saida jiragen akan kudi dalar Amurka miliyan 25 amma sai masu sayen suka coge kan sai dai dalar Amurka miliyan 11.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa fadar shugaban kasar a watan Oktobar shekarar 2016 ta fitar da shelar neman masu sayen jiragen biyo bayan umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Source :naij hausa
Title :
Haryanzu Buhari Bai Cika Alkawarin Saida Jiragen Sa Dayace Zaiyi Ba
Description : Jiragen alfarma na shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari guda biyu da yayi alkawarin sayarwa domin tattalin kudin kasa na Falcon 7X da ku...
Rating :
5