Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya ce damokradiyar kasar na ja da baya sannan kuma ba aibu bane don sojoji sunyi juyin mulki.
Ekweremadu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayinda yake bayar da gudunmawarsa a wani fafatawa da sanatan dake wakiltan Kogi ta tsakiya Ahmed Ogembe ya shirya.
Ogembe yayi zargin cewa Yahaya Bello, Gwamnan jihar Kogi, ya yi hayan yan iska domin su hargitsa wani shirin tallafi day a shirya a mazabarsa.
Ya kawo misalai daban-daban na inda aka ci zarafin yan majalisar tarayya, inda yayi gargadin cewa kada a kuskura ayi wasa da damokradiyar kasar.
Ekweremadu ya kuma fada ma gwamnan jihar Kogi cewa hanyar day a dauka ba mai billewa bane.
Source :naij hausa
Title :
Haryanzu Bamu Bar Zamanin Juyin Mulki Ba-Ekweremadu
Description : Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya ce damokradiyar kasar na ja da baya sannan kuma ba aibu bane don sojoji sunyi juyin...
Rating :
5