1- Kada ka dogara ga hotunan da ba na gaskiya ba ne.
Misali na neman taimako akan girgizar ƙasa, muna ganin iyalai tsaye gaban ɓaraguzan gidajen su cikin damuwa yayin da su ke jiran a kawo musu dauki.
Kananan yara su suka fi ban tausayi ta yadda su ke murmushi idanuwan su sun yi ƙwala-ƙwala.
Dalilin haka shi ne ba zamu taba ƙyale wadannan yara ba.
Sai dai wasu bincike daban daban da aka gudanar sun nuna cewa irin wadannan hotunan ba su cika shawon kan jama'a ba kamar yadda ake fata.
Masu bincike a jami'ar Alberta sun tambayi wasu mutane da su ziyarci shafin Internet da aka ƙirkira wanda ya bada zabin daukar dawainiyar ƙananan yara ko iyalai da rubtawa ƙasa ko balai'in tsunami ya abka musu.
A wasu shafukan, an sanya hotunan ƙananan yara kyawawa yayin da a wasu kuma matsakaita.
Yayin da bayanan da ake rubutawa da hotunan suka yi nuni da cewa yaron ya rasa gidan su ko kuma iyayensa sakamakon bala'in daya abku, hotunan yaron ba zai sa wani abu ya sauya ba.
Amma matuƙar yanayin bai yi muni ba, yaran da suke ƙyawawa basu cika samun yadda suke so ba.
Wasu na ganin cewa irin wadannan yaran suna da basira kuma za su iya taimakawa kansu da kansu.
Masu wallafa littafin sun bada shawarar cewa idan ƙungiyoyi bada agaji na neman samun kudade, ya kamata su yi amfani da hotunan da ba za su riƙa sa mutane dariya ba sosai.
Mun fi bada gudummawa saboda wani bala'i idan muka ga mutanen da lamarin ya rutsa da su na ƙokarin sake fara rayuwar su
Ya na taimaka wa idan mutanen da ke hotunan suka nuna ƙwarin guiwa maimakon nuna cewa tamkar sun yanke ƙauna.
A wani bincike da ta gudunar a jami'ar Royal Holloway da ke Landan, Hanna Zagefka ta gano cewa hankulan mutanen sun fi karkata ta fuskar son su bada tallafi bayan abkuwar wani bala'i, fiye da abkuwar yakin basa-sa saboda suna ganin mutanen da lamarin ya rutsa da su ba su da laifi.
Sai dai kuma sun fi bada taimako sosai da zarar mutanen suka nuna cewa sun yunƙuro domin su taimaki kansu, maimakon jiran a zo don a taimaka musu.
Darasin da za'a dauka anan shi ne na amfani da hotunan iyalai da ke ƙokarin sake gina gidan su.
Misali, maimakon hotunan mutane na zaune suna jiran a kawo musu tallafi.
2-Kada ka maida hankali ga labarin dai-dai-kun mutane.
A duk lokacin da wani babban bala'i ya abku, yana da wahalar gaske a iya kimanta ainihin abun da ke faruwa a wurin, a don haka masu neman taimako su kan bada labarin wani mutum da lamarin ya rutsa da shi saboda yana taimaka wa wajen gano mutanen da al'amari ya shafa.
Mai yiwuwa hakan abu ne mai kyau, domin mu kan ji kamar mu ne abun ya shafa inda muke tuna irin mawuyacin halin da suka shiga, har mu bada gudummuwar kudi da fatan zai taimaka wajen rage musu wahalhalun da suke ciki.
Sai dai a yanzu, mu kan ji labaran wasu dai-dai-kun jama'a ne da har ta kaiga yanzu irin wannan yanayi bai wani tasiri a gare mu.
Abun da ƙungiyoyin farar hula su ke buƙata shi ne su samu masu basu gudummuwa saboda tasirin ayyukan da ƙungiyoyin ke yi maimakon gudummuwa saboda labarin mawuyacin halin da wani mutum guda ya shiga ciki.
Don haka a wasu lokuta ya kamata ƙungiyoyin bada agaji su maida hankali wajen abubuwan da ke faruwa.
Masana halayyar dan adam a ƙasar Israila sun horas da wasu mutane 300 inda suka ba su labarin matsalar ƙaranci kudade da wata cibiyar da ke inganta rayuwar mutanen da hadarin mota ya rutsa da su ke ciki.
An dai raba mutanen rukuni-rukuni, inda kowane rukuni aka ba su labarai iri daban daban.
An shaida wa rukunin farko cewa kudaden da ake bukata domin taimakawa wata mata ce da mummunar hadarin mota ya rutsa da ita, yayin da sauran rukunonin kuma aka shaida musu cewa kudaden domin a taimaki wani mutum ne daya ji rauni.
Sauran kuma aka ce musu za'a taimaki wasu mutane maza ne ko kuma mata a cibiyar ba tare da an yi musu ƙarin bayani akai ba.
Samun gudummuwa ya dogara ne ga yadda aka nemi taimako
Akasarin mata sun ce a shirye suke su bada gudummuwar dala $35 domin taimakawa wata mace da hadarin mota ya rutsa da ita, yayin da su ke da niyyar bayar da dala $16 kacal domin taimakawa daukacin matan baki daya.
Amma kuma mazajen sai suka ce zasu fi bada taimako ga daukacin matan maimakon wata mace guda ko namiji guda.
Sai dai kuma lamarin ya sauya bayan da aka shaida musu cewa mazaje ne za'a taimake su.
Wato dai kusan duk masu bada gudummuwar idan suna da alaka da mutanen, sun fi bada gudummuwa da yawa bayan da aka shaida musu cewa gudummuwar da ake bukata ta mutum guda ne ba wasu gungun mutane maza ko mata ba.
Abun da ya kamata ƙungiyoyin bada agaji su yi idan za su iya shi ne, su gano ko masu bada agaji za su fi son bayarwa idan wanda ake bukatar taimakon yana da alaka da su.
Idan kuma ba haka ba ne, su nemi gudummuwa domin magance wata matsala ko kuma inganta rayuwar al'umma zai fi yin tasiri.
3- Yi nazari sosai wajen amfani da kalmomin da suka dace
Sauya wata kalma za ta iya yin tasiri wajen samun gudummuwa ga ƙungiyoyin bada agaji.
Masanin halayyar dan adam Nicolas Gueguen ya gudanar da wani bincike a wasu gidajen da ake yin biredi da sauran kayan ƙwalam har su 14 a Burtaniya.
An ajiye asusu daban daban akan tebur inda a jikin kowane asusu aka rubuta bayanai game da ƙungiyar bada agaji da ke ƙasar Togo.
Kusan bayanan da aka rubuta a dukkan asusun sun yi kama da juna, illa dai akwai wata kalma guda.
Gudummuwa= Soyayya
Gudummuwa= Taimako
Gudummuwa
Bayan da masanin halayyar dan adam ya ƙidiya kudaden da aka sanya a kowane asusu, an gano cewa asusu da aka rubuta kalmar ''Soyayya" kudin da ke ciki ya rubanya wanda ke asusu da aka rubuta kalmar ''Taimako".
Masu binciken su ka ce kalmar ''Soyayya" kan ja ra'ayin mutane su nuna ƙauna tare da goyon baya wanda kuma ya ke sa mutane su bada gudummuwa.
4- A sanar da bayar da gudummuwa ga jama'a
Kowne mutum na son a riƙa nuna shi a matsayin mutum mai alheri.
A shekarar 2010 an gudanar da wani bincike na wasu gungun mutane a Japan da aka basu kudi aka buƙace su akan ko su ajiye duk kudin ko kuma suna iya bada kyauta ga wasu ƙungiyoyin agaji da aka gabatar da jerin sunayen su.
Sakamakon ya nuna cewa mutanen sun fi son bada gudummuwar kudi idan mutumin da ke gaban su yana kallon su ta talbijin.
Alheri abu ne mai kyau - muna iya bada kyauta mai yawa idan muna tunanin za'a kwatanta mu da wasu
5- Idan kana son kudi a hannun attajirai, kada ka nuna kamar akwai wani abu nasu
A lokacin da ƙungiyoyin bada agaji suka gabatar da ƙoƙon barar neman taimako, wasu lokuta su kan yi ƙokarin shawo kan masu bada gudummuwa cewa yin hakan abu ne mai kyau gare su da kuma kamfanonin su, musamman idan da za su bada gudummuwa mai tsoka.
Sai dai wani bincike da aka gudanar a ƙasar Netherland ya nuna cewa wannan dabara ta na iya cin karo da cikas.
Source :bbc hausa