Bisa dukkan alamu Sanata Chris Ngige wanda shi ne Ministan kwadago na kasar nan ya cin ma matsaya da Ma’aikatan Jami’a da ke yajin aiki tun bara bayan wani taro da aka yi a Garin Abuja.
Chris Ngige ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai biya Ma’aikatan Makarantun jami’ar wasu Naira Biliyan 8 domin kawo karshen wannan yajin aiki. Yanzu haka Kungiyoyin NASU da SSANU da NAAT duk su na yaji tun bara.
Ministan kasar Ngige da kuma karamin Ministan ilmi Farfesa Anthony Anwukah su ka sa hannu a takardar yarjejeniyar inda a bangaren Ma’aikatan Gwamnatin kuma Shugaban NAAT da kuma Kungiyar SSANU da Sakataren NASU su ka sa hannu.
A cikin wannan kudin da za a saki, za a biya Malaman Jami’a na ASUU na jami’ar Ilorin da ta Nsukka da ba su cikin wadanda aka biya alawus a baya. Ana sa rai a gobe za a janye yajin aikin inda ayyuka za su dawo bakin aiki kamar ba ayi ba a cikin Jami’o’in.
Source :naij hausa
Title :
Gobe Ma'aikatan Jami'a Zasu Janye Dogon Yajin Aikin Da Sukeyi
Description : Bisa dukkan alamu Sanata Chris Ngige wanda shi ne Ministan kwadago na kasar nan ya cin ma matsaya da Ma’aikatan Jami’a da ke yajin aiki tun ...
Rating :
5