A yayin ganawa da manema labarai na mujallar karshen mako ta kamfanin jaridar Daily Trust, fitaccen jarumi kuma shugaban cibiyar jaruman hausa, Alhassan Kwalli, ya yi karin haske dangane sa wasu al'amura da suka shafi sana'ar su ta shirya fina-finai.
Jarumin dai ya bayyana cewa, babbar manufa ta wannan cibiya a matsayin sa na jagoranta shine tabbatar da hadin kai a tsakanin dukkan jarumai tare da kare hakkokin su a fagen sana'ar su.
Alhassan Kwalli ya ci gaba da cewa, ya yi matukar murna da wannan ganawa ta sa da 'yan jarida inda ya hikaito ma su irin ci gaba da su ke samu a fagen sana'ar su da a yanzu sun zamto tamkar madubin dubawa na rayuwar al'umma.
Fitaccen jarumin yake cewa, ba bu shakka fina-finan su sukan haskaka al'adun hausawa wanda a yanzu sun zamto kwatankwacin rayuwar su.
A yayin tuntubar sa dangane da yadda gwamnati ke mu'amalantar su, Jarumi Alhassan Kwalli ya bayyana cewa, ko shakka ba bu akwai kyakyawar fahimta da kuma alaka mai karfin gaske tsakanin su da gwamnati.
Source :naij hausa
Title :
Fina Finan Mu Kwatance Ne Na Rayuwar Al Umma - Alhassan Kwalle
Description : A yayin ganawa da manema labarai na mujallar karshen mako ta kamfanin jaridar Daily Trust, fitaccen jarumi kuma shugaban cibiyar jaruman hau...
Rating :
5