Mun samu labari daga Daily Trust cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta damke Jami’in bada agajin gaggawa da yayi gaba da kayan ‘Yan gudun hijira inda yanzu har an shiga Kotu.
Ana zargin Shugaban da wasu Jami’an Hukumar SEMA mai bada agajin gaggawa a Jihar Gombe Danlami Arabs Rukuje da karkatar da kayan Bayin Allah da ke sansanin gudun hijira. Yanzu haka dai an dage shari’ar sai Afrilu.
EFCC na karar Rukuje da ma’aikatan da ke tsare dakin ajiyar kayan da sace wasu kayan gini na ‘yan gudun hijira. Kayan da aka sace sun hada da buhunan siminti 5000 da kayan fenti da sauran kayan da aka kawo domin jama’an.
Kwamitin da Shugaban kasa Buhari ya nada domin kula da mutanen da ke gudun Hijira a Yankin Arewa maso gabas ne ta kawowa Hukumar wannan kaya amma aka sace. Yanzu dai wadannan Ma’aikata su na neman Kotu ta ba su beli.
Source :naij hausa
Title :
EFCC Sun Damke Wadanda Sukayi Awun Gaba Da Kayan Yan Gudun Hijira
Description : Mun samu labari daga Daily Trust cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta damke Jami’in bada agajin gagg...
Rating :
5