Wata babbar kotun kasar India dake jihar Jharkhand ta yankewa wasu mutane 11 hukuncin daurin rai da rai, saboda kama su da aka yi da kisan wani musulmi saboda yana tallar naman shanu a shekarar da ta gabata.
Mutanen sun lakadawa Alimuddin Ansari, mai shekaru 55, dukan tsiya, inda har sai da ya rasa ransa, saboda kawai sun same shi yana sayar da naman shanu.
Wannan shine karon farko da gwamnatin India ta yanke hukunci akan mutanen da suke sanya ido akan masu cin naman shanu, duk kuwa da cewa an shafe shekaru da yawa ana samun kai hare hare akan musulmai masu sayar da naman.
Wanda suke bin addinin Hindu sun dauki Saniya a matsayin wata halitta mai tsarki wanda har ya kai ga mawar da wasu suna bauta mata, sannan kuma suka haramta kisan ta a da dama daga cikin jihohin kasar ta India, ciki kuwa har da jihar Jharkhand.
Sau da yawa masu bautar saniyar suna kai hare hare akan masu cin naman shanu da kuma masu sayar dashi a kasar ta India, sannan kuma hukuma bata fiya daukan mataki akan wanda ta kama da laifin kai harin ba.
Source :naij hausa
Title :
Duk Wanda Ya Kashe Musulmi Za'a Yanke Mar Hukuncin Daurin Rai Da Rai - Kotu
Description : Wata babbar kotun kasar India dake jihar Jharkhand ta yankewa wasu mutane 11 hukuncin daurin rai da rai, saboda kama su da aka yi da kisan w...
Rating :
5