Wani dalibi dan 400L a jami’ar jihar Abia da ke garin Uturu, mai suna Princewill Okechukwu, yace ya shiga kungiyar asiri ne a cikin jami’a, saboda cika burinsa na zama dan siyasa bayan gama makaranta.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Okechukwu yana daya daga cikin wadanda ake zargi su biyar da hukumar ‘Yan Sanda ta tasa keyarsu a ofishin ma’aikatan na Umuahia, bisa ga zargin harkokin kungiyar asiri da kuma fashi da makami.
Jaridar naij ta samu labarin cewa wadanda ake zargin kwamishinan ‘Yan Sanda, Anthony Ogbizi, ne ya tasa keyar su ne a ranar Litinin, 26 ga watan Maris, a jihar.
Dalibin makarantar wanda yake aji na karshe a jami’a, mai shekara 22, wanda ke karantar nazarin kimiyyar siyasa, shine shugaban kungiyar mai suna Black Axe a jami’ar.
Wanda ake zargin yace, ya kasance a cikin kungiyar shekara daya knan, yayi nadamar cewa idan har an sakeshi bazai sake komawa harka da kungiyar asiri ba.
Wata mace da aka kama tare dasu mai suna Chika, ta nuna cewa an kamata ne bisa kuskure dan tana jiran wani ne a kusada wurin lokacin da aka kamata.
Source :naij hausa
Title :
Dalilin Dayasa Nashiga Kungiyar Asiri
Description : Wani dalibi dan 400L a jami’ar jihar Abia da ke garin Uturu, mai suna Princewill Okechukwu, yace ya shiga kungiyar asiri ne a cikin jami’a, ...
Rating :
5