Wata babban kotu da ke zaune a Abuja a jiyar Laraba, ta bada belin Maryam Sanda wacce ke garkame a kurkuku da laifin kisan mijinta, Bilyamin Bello, wanda dan tsohon shugaba jam’iyyar PDP ne.
Jastis Yusuf Halilu wanda ya ki bada beli a baya ya bayyana cewa akwai wani dalili kwakkwara da ya gamsar da shi kuma ya sa ya bada belin.Alkalin ya ce rahoton asibiti ya nuna cewa Maryam na cikin wani mugun hali da jami’an fursunonin ba zasu iya kula da ita ba.
Justis Halilu ya kara da cewa ya gamsu ne saboda banda cewa tanada juna biyu, tana fama da ciwon Asthma.
Kana lauyoyin gwamnati sun gaza karyata cewa kayayyakin kiwon lafiyan da ke fursunonin ba zai taimakawa wajen kula da Maryan Sanda ba.
Daga karshe, kotu ta bata beli kuma kaidar belin shine mutane 2 su tsaya mata da kuma wani dukiya a Abuja. Kuma an dakatad da karar zuwa ranan 19 ga watan Maris.
Source :naij hausa
Title :
Dalilin Dayasa Kotu Ta Saki Maryam Sanda
Description : Wata babban kotu da ke zaune a Abuja a jiyar Laraba, ta bada belin Maryam Sanda wacce ke garkame a kurkuku da laifin kisan mijinta, Bilyamin...
Rating :
5