Rahotanni sun kawo cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya sanar da cewa ya yanke hukuncin bin matakin sulhu day an ta’addan Boko Haram a maimakon karfin soja wajen ceto 'yan matan Dapchi da aka sace ne domin ganin cewa babu daya daga cikinsu da ta rasa ranta.
Buhari ya yi wannan ikirari ne a yayinda ya hadu da 'yan matan a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Alhamis, 22 ga watan Maris.
Shugaban kasar ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ta dauki matakin samar da isasshen tsaro a makarantun kwana domin guje ma sake afkuwar wannan lamari..Ya sha alwashin ladaftar da duk wani jami'in tsaron da ya yi sakaci da aikinsa ta yadda har zai ba mayakan Boko Haram damar sake sace wasu dalibai. Shugaban ya kuma nuna cewa a shirye gwamnati take ta yafewa duk wani dan ta'adda da ya ajiye makami yah au tudun tuba.
A yanzu haka a yayin da ake murnar dawowar yan matan Dapchi guda 104 da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta sako a ranar Laraba 21 ga watan Maris, su kuwa iyayen yan matan Chibok kokawa suka yi.
Guda cikin Iyayen yan matan Chibok, Ayuba Alamson ya bayyana cewa gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari bata da wani kwakkwaran shirin kwato musu yayansu daga hannun Boko Haram.
Source :naij hausa
Title :
Dalilin Dayasa Ban Sulhunta Da Boko Haram Ba - Buhari
Description : Rahotanni sun kawo cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya sanar da cewa ya yanke hukuncin bin matakin sulhu day an ta’addan Boko Haram a maim...
Rating :
5