Idan ba ku manta ba Manyan Arewa sun bayyana cewa ba dole bane su zabi Shugaba Buhari idan ya fito takara a 2019 ba. Sai ga shi kuma yanzu Inyamurai sun bayyana cewa babu ruwan su da shi a zabe mai zuwa.
Manyan Kasar Inyamurai sun bayyana cewa fau-fau ba su ba Shugaba Buhari a 2019, kuma ba mulkin kasar nan su ke hari a 2023 ba. Inyamuran kasar su kace abin da su ke so shi ne ayi wa Najeriya garambawul su ka kuma nemi Shugaba Buhari ya sauka a 2019.
Inyamuran kasar sun bayyanawa Jaridar Vanguard wannan inda su kace dadin bakin da ake kokarin yi masu na tayin karbar mulkin Najeriya ba zai yi aiki ba. Shugabannin Inyamuran su kace garambawul kawai za ayi don kowa ya zama daidai a kasar amma ba mulki ba.
Shugaban Sanatocin Yankin kasar Ibo Enyinninya Abaribe yace babu ruwan su da wani mulkin Najeriya a wannan tsarin da ake tafiya a kai yau.
Shugaban Kungiyar Oganaeze Cif Emeka Attamah yace ba za su marawa wani ‘dan siyasa baya ba domin su ba siyasa su ke yi ba.
Source :naij hausa
Title :
Dadin Bakinka Bazaisa Mu Zabe Ka Ba-Inyamurai Ga Buhari
Description : Idan ba ku manta ba Manyan Arewa sun bayyana cewa ba dole bane su zabi Shugaba Buhari idan ya fito takara a 2019 ba. Sai ga shi kuma yanzu I...
Rating :
5