Tsohuwar shahararriyar jarumar nan ta kamfanin shirya fina-finan Hausa, Fati Muhammad ta caccaki auren yar gwamnan jihar Kano, Fatima Ganduje wanda akayi a makon da ya gabata.
A cewar Fati da ace yar fim ce ta aikata tsiyar da akayi a bikin yar Ganduje da an zage su tare da yi masu tofin Allah tsine.
Ta bayyana su a matsayin azzalumai kawai, sannan ta ce inda Rahma Sadau ko Ummi Zee Zee ne suka yi haka da tuni a soke su.
Ta kuma yi ba’a inda ta ce ina yan Hizbah suke, kodai dama aikinsu akan marasa gata suke yi.
Daga karshe Fati ta ce Ganduje ya ci amanar Musulunci dominana masa kirari da khadimul islam.
Source :naij hausa
Title :
Da Yar Film Ce Tayi Abinda Yar Ganduje Tayi Da Yanzu Haka Ana Tsine Mata-Fati Muhd
Description : Tsohuwar shahararriyar jarumar nan ta kamfanin shirya fina-finan Hausa, Fati Muhammad ta caccaki auren yar gwamnan jihar Kano, Fatima Ganduj...
Rating :
5