Jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaci jam'iyya mai mulki, APC, da gwamnatin tarayya da su daina yaudarar jama'a da yaki da cin hanci, sannan su dawo da kudin da suka sata bayan hawansu mulki.
Jam'iyyar PDP ta ce yaki da cin hanci da shugaba ke yi babu gaskiya balle adalci cikinsa domin dukkan gwamnonin da suka yi masa yakin zabe a 2015 da kuma yanzu suke kewaye da shi, sun yi amfani da kudin jama'a ne wajen tallafa masa.
Sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, a wata sanarwa da ya fitar jiya, ya ce, babu wata shaida dake nuna cewar jam'iyyar PDP tayi almubazzaranci da kudin jama'a tare da bayyana cewar, 'yan Najeriya sun san da biliyoyin jama'a aka yiwa jam'iyyar APC yakin neman zaben 2015.
Ologbondiyan ya kara da cewar, ya kamata gwamnatin APC ta daina neman kudin da take cewa an sace domin kudin na hannun 'ya'yanta.
Kazalika jam'iyyar PDP ta bayyana cewar, tunda aka fara siyasa a Najeriya, ba a taba samun jam'iyyar da ta kashe makudan kudi a yakin neman zabe kamar APC ba, tare da bayyana cewar dukkan kudaden an same su ne ta gurbata ciyar hanya, daga hannun gwamnonin jam'iyyar PDP da suka canja sheka zuwa jam'iyyar.
Source :naij hausa
Title :
Cin Moriyar Kudin Da Aka Sata Daga Gwamnatin Nijeriya Buhari Yakeyi - PDP
Description : Jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaci jam'iyya mai mulki, APC, da gwamnatin tarayya da su daina yaudarar jama'a da yaki da cin hanci,...
Rating :
5